PDP Ta Sauya Wurin Babban Taronta Daga Kano Zuwa Ibadan, Ta Kuma Dage Zaben Shugabanninta

Abuja – Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yanke shawarar sauya wurin da za ta gudanar da babban taronta na kasa daga Kano zuwa Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Har ila yau, ta dage ranar zaben shugabannin jam’iyyar zuwa Nuwamba 2025.
Canjin Tsari da Kwanan Watan Taron
Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa taron zaben shugabannin jam’iyyar zai gudana ne a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba 2025 a Ibadan maimakon Kano kamar yadda aka tsara tun farko.
Ya kara da cewa jam’iyyar ta amince da wannan canjin ne bayan taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC) da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis. A baya, an tsara taron ne domin gudana a watan Agusta 2025 amma aka dage shi zuwa Nuwamba saboda wasu dalilai.
Shirye-shiryen Taron
Ologunagba ya bayyana cewa duk shirye-shiryen taron za a kammala su a taron NEC na gaba wanda zai gudana a ranar Litinin, 25 ga Agusta 2025. An kuma umarci shugaban jam’iyyar na kasa da sakataren jam’iyyar na kasa da su sanar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) game da shirin taron zaben.
Jam’iyyar ta kuma amince da membobin kwamitin shirya taron da kuma kwamitin rabon mukamai (ZC) domin tabbatar da gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.
PDP Ta Warware Rikice-rikicen Cikin Gida
Sakataren yada labaran ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar sun nuna gamsuwa da yadda aka warware wasu rikice-rikicen cikin gida, wanda ke nuna cewa PDP ta fara samun hadin kai da kuma tsayayya.
“PDP na nan daram da hadin kai, kuma za ta ci gaba da zama madogara mai inganci ga al’ummar Najeriya,” in ji Ologunagba. Jam’iyyar tana da burin kwato mulki daga All Progressives Congress (APC) a zaben 2027.

Matakin Kare Amanar ‘Yan Najeriya
A wani muhimmin mataki, NEC ta umarci Kwamitin Aiki na Kasa (NWC) da ya fara shirin gurfanar da tsoffin mambobin PDP da suka lashe zabuka amma suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu.
“A kokarinta na kare amanar ‘yan Najeriya da suka zabi PDP, NEC ta umurci NWC da ya dauki matakin doka domin kwato kujerun dukkanin ‘yan majalisar tarayya da na jihohi da suka lashe zabe a jam’iyyar PDP amma suka sauya sheka.”
An kara da cewa, bisa ga sashe na 68 (1)(g) da kuma 109 (1)(g) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wadannan mambobin sun rasa kujerunsu saboda sauya sheka.
Shirin PDP Domin Zaben 2027
A wani labari, an bayyana cewa waɗanda suka kafa PDP a shekarar 1998 sun bayyana matsayarsu kan wanda ya kamata a tsayar takarar shugaban ƙasa a zaben 2027.
A wani taron da suka gudanar a Abuja, jiga-jigan PDP sun amince a ɗauko ɗan takara daga Kudancin Najeriya domin tabbatar da adalci da daidaito a jam’iyyar.
Farfesa Jerry Gana ya kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin APC da cewa ta kawo talauci da rashin tsaro maimakon alkawuran da ta yi na kawo canji a Najeriya.
Jam’iyyar PDP tana kokarin dawo da hadin kai da karfafawa mambobinta gwiwa domin fafatawa da APC a zaben 2027.
Asali: Legit.ng








