Gwamnatin Jihar Neja Ta Fara Ginin Titi Mokwa-Rabba Kan Naira Biliyan 7
Ambaliya Ta Haddasa Asarar Rayuka da Dukiya
Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tabbatar da cewa ambaliyar ta yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma lalata kadarori da aka kiyasta darajarsu da miliyoyin naira.
Gwamna Bago ya bayyana cewa aikin zai hada da gina gada hudu da za su tabbatar da tsaron hanya da saukaka zirga-zirga a tsakanin Mokwa da Rabba.
Matakan Gaggawa Don Dakile Bala’o’i a Gaba
Gwamnan ya umarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati (MDAs) da su gudanar da cikakken bincike a kan hanyoyin ruwa da tsarin kasa, da nufin tantance yankunan da ke cikin hadari domin daukar matakin sauya mazauni daga bakin ruwa.
Ya ce wannan mataki ne na rage yawan afkuwar irin wannan ibtila’in a nan gaba da kuma kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.
Rarraba Kayan Tallafi da Ziyarar Rabba
A lokacin ziyarar, Gwamna Bago ya raba kayan agaji na gaggawa ga gidaje da dama da ambaliya ta shafa. Haka kuma ya ziyarci Rabba inda ya duba gada da ambaliya ta yanke, ya kuma bada tabbacin cewa aikin zai farfado da hanyar tare da dawo da tattalin arzikin yankin.