“Yan Arewa Ku Ba Tinubu Damar Wa’adi Na Biyu Kamar Yadda Kuka Yi Wa Buhari”

“Yan Arewa Ku Ba Tinubu Damar Wa’adi Na Biyu Kamar Yadda Kuka Yi Wa Buhari”

Spread the love

“A Taimaka Masa Kamar Buhari”: Hadimin Tinubu Ya Roƙi ‘Yan Arewa Alfarma

Onanuga Ya Ce Tinubu Ya Cancanci Wa’adi Na Biyu

Abuja – Hadimin shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya yi kira ga ‘yan Arewa su ba shugaban kasa damar kammala wa’adinsa na biyu kamar yadda aka yi wa marigayi Muhammadu Buhari.

A cewar Onanuga, ana yunƙurin rage darajar Tinubu saboda asalinsa dan Kudu ne, ba don wani dalili na gaskiya ba. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da jaridar Vanguard a ranar Laraba.

Bayo Onanuga yana roƙon 'yan Arewa su ba Tinubu dama kamar Buhari
Bayo Onanuga yana roƙon ‘yan Arewa su ba Tinubu dama kamar yadda aka yi wa Buhari. Hoto: Twitter

Kira Ga ‘Yan Siyasar Arewa

Onanuga ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da su yi hakuri, su bar Kudu ta kammala wa’adinta na mulki, yana mai cewa Kudu ma ta yi hakuri lokacin mulkin Buhari.

“Wannan shugaban kasa dan Najeriya ne, ya cancanci wa’adi biyu kamar yadda Buhari ya samu,” in ji Onanuga. “Ka da mu sadaukar da kasa saboda son rai.”

Zargin Nuna Bambanci

Hadimin shugaban kasa ya karyata zargin nuna wariya ga Arewa, yana mai cewa ana kokarin rage karfin Tinubu saboda asalin sa dan Kudu ne.

Ya ce mukamai masu muhimmanci a harkar tsaro suna hannun ‘yan Arewa, kuma tsaro ya inganta a wurare irin su Birnin Gwari da Igabi.

Ayyukan gwamnatin Tinubu a Arewa
Hadimin Tinubu ya ce mai gidansa ya cancanci wa’adi na 2. Hoto: Facebook

Matsayin ‘Yan Arewa A Gwamnati

Game da zargin fifita yankin Kudu maso Yamma wajen nade-naden gwamnati, Onanuga ya kalubalanci masu zargi da su kawo hujja ta lissafi, ba kalmomi kawai ba.

Ya kuma ce ba gaskiya ba ne cewa an yi watsi da ayyukan Arewa, domin gwamnatin Tinubu ta gaji manyan ayyukan da aka bari babu kammalawa.

Mukamai Masu Muhimmanci

Onanuga ya kawo hujja da mukaman tsaro da ‘yan Arewa ke rike da su, yana mai cewa hakan na nuna adalci a nade-naden gwamnatin Tinubu.

“Kuna bukatar daidaitattun kididdiga. Wannan siyasa ce kawai don rage karfin shugaban kasa. Akwai tituna marasa kyau a ko’ina, ba Arewa kadai ba.

“Mai Ba da Shawara kan Tsaro, Shugaban Rundunar Soji, da Ministocin Tsaro duka ‘yan Arewa ne. Birnin Gwari da Igabi sun fi samun zaman lafiya yanzu.

“Na bi hanyar Kaduna zuwa Abuja ba tare da hadari ba, wanda a da ba zai yiwu ba.”

– Bayo Onanuga

Alkawuran Tinubu Ga Arewa

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya tabbatar cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya cika alkawuransa ga yankin Arewa.

Idris ya bayyana cewa yankin Arewa bai bin Shugaba Tinubu bashi kan alkawuran da ya dauka kafin zaben 2023.

Haɗin Kai Tsakanin Yankuna

Ministan ya nuna cewa shugaban kasa ya saka ‘yan Arewa masu yawa a cikin gwamnatinsa domin yin aiki tare da shi, akasin zargin wasu mutane.

Ya kara da cewa gwamnatin Tinubu ta ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba a duk fadin kasar, ba tare da nuna wariya ga kowane yanki ba.

Asali: Legit.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *