Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 171, Ta Kashe Mutane Huɗu a Jihar Gombe
Gombe – Mummunar ambaliyar ruwa da ta biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin watanni biyu ta yi barna sosai a jihar Gombe, inda ta lalata gidaje 171 kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutane huɗu, galibinsu ƙananan yara ne.

Rahoton Lalacewa da Asarar Rayuka
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta bayyana cewa ambaliyar ruwa ta shafi kananan hukumomi hudu a jihar – Dukku, Kwami, Gombe da Akko. Haruna Abdullahi, shugaban hukumar SEMA, ya bayyana hakan yayin da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis.
“Ya zuwa yanzu, mun tattabatar da lalacewar gidaje 87 a Dukku, 27 a Kwami, 30 a Gombe da kuma 27 a Akko, wanda ya haɗa da wata coci. Wannan ne ya sa muke ta yin kira ga mazauna jihar da su kula da gyaran muhalli, musamman share magudanan ruwa.”
– Haruna Abdullahi, Shugaban SEMA Gombe
Tallafin SEMA Ga Wadanda Abin Ya Shafa
Domin magance matsalar, hukumar SEMA ta yi shirin kai gudummawar abinci da sauran kayan masarufi ga wadanda ambaliyar ta shafa. Haruna ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su daina zubar da shara a magudanan ruwa, wanda ke haifar da ambaliya.
Ya kuma yi gargadin cewa iyaye su sa ido sosai kan ‘ya’yansu yayin da ake ruwan sama, saboda yawancin wadanda suka mutu a sakamakon ambaliyar ruwa ƙananan yara ne.

Gargadin Kan Sare Bishiyoyi
Shugaban SEMA ya kuma yi kakkausar suka ga yadda ake sare bishiyoyi a jihar domin yin gawaki ko iccen girki. Ya bayyana cewa wannan aikin yana haifar da kwararar hamada wanda ke kara yawan ambaliya.
Ya shawarci mazauna jihar da su daina sare bishiyoyi, maimakon haka su kara dasa sabbin bishiyoyi, musamman a kusa da gidajensu, domin rage tasirin iska da ambaliya.
Barnar Ambaliya a Sauran Jihohi
Bayanin da aka fitar daga baya ya nuna cewa ambaliyar ruwa ta yi barna a jihohi 31 a Najeriya a shekarar 2024, inda ta lalata gonaki 180,000 kuma ta shafi rayuwar mutane miliyan 1.2. Kimanin mutane miliyan 2.2 ne suka rasa matsugunansu sakamakon wannan bala’i.
Wannan lamari ya haifar da karuwar farashin kayayyaki a kasuwa, wanda ke dagula talauci a fadin kasar.
Abubuwan Da Mazauna Gombe Za Su Yi Domin Kaucewa Ambaliya:
- Kauracewa zubar da shara a magudanan ruwa
- Gyara magudanan ruwa kai tsaye
- Dasa bishiyoyi masu yawa
- Kula da yara yayin ruwan sama
- Yin amfani da wuraren zubar da shara da gwamnati ta tanada
Hukumar SEMA ta kuma yi kira ga kowa da kowa da ya taimaka wajen rage illolin ambaliyar ruwa ta hanyar bin ka’idojin kiyaye muhalli.
Asali: Legit.ng