Jam’iyyar ADC Ta Dakatar Da Dan Majalisar Wakilai Leke Abejide Kan Zargin Rashin Biyayya
Dakatarwar Ta Zo Bayan Zargin Gudanar Da Taron Sirri Ba Tare Da Izinin Shugabanni Ba
Reshen jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Kogi ya sanar da dakatar da dan majalisar wakilai Hon. Leke Abejide daga ayyukan jam’iyyar har abada. Dakatarwar ta zo ne bayan zargin gudanar da taron sirri ba tare da izinin shugabannin jam’iyyar ba da kuma yunkurin jan ra’ayin wasu membobin jam’iyyar zuwa hadaka da All Progressives Congress (APC).

Sanarwar Dakatarwa
Sakataren ADC na jihar Kogi, Adaji John, ya fitar da sanarwar dakatarwar a ranar Juma’a a Lokoja. A cikin sanarwar, jam’iyyar ta zargi Hon. Abejide da “matsanancin rashin ladabi” da kuma “aikata ayyuka na adawa da jam’iyya.”
“Jam’iyyar ADC reshen jihar Kogi ta dakatar da ɗaya daga cikin wakilanmu a majalisar tarayya. Wanda abin ya shafa shi ne Hon. Leke Abejide, wanda ke wakiltar mazabar Yagba ta Gabas da Yamma da Mopamuro,” in ji sanarwar.
Dalilan Dakatarwar
Bayanin ya nuna cewa dakatarwar ta samo asali ne bayan Hon. Abejide ya gudanar da wani taron sirri da wasu ‘yan jam’iyya a Abuja ba tare da sanin ko amincewar shugabannin ADC a jihar ba. Taron ya haifar da cece-kuce a cikin jam’iyyar.
Adaji John ya bayyana cewa:
“Domin karin haske, an dakatar da Hon. Abejide ne bayan an tabbatar da laifin rashin biyayya ga shugabanni da kuma yunƙurin kwace ikon shugaban jam’iyya da sakatare na jiha.”
Zargin Hadaka Da APC
Jam’iyyar ta kuma zargi dan majalisar da yunkurin jan ra’ayin shugabannin ADC a matakin ƙananan hukumomi da mazabu domin su mara wa APC mai mulki baya. Wannan matakin ya saba wa manufar jam’iyyar ADC.

“Hon. Abejide ya zarce gona da iri lokacin da ya yi yunƙurin jan ra’ayin shugabannin jam’iyya a mazabu da ƙananan hukumomi zuwa wani taro da nufin hada hannu da APC a maimakon ADC,” in ji sanarwar.
Martanin Dan Majalisar
A baya, Hon. Abejide ya yi ikirarin cewa shi ne mai ɗaukar nauyin ADC a jihar Kogi. Ya bayyana cewa yana da ‘yancin sauya sheƙa zuwa APC a duk lokacin da ya ga dama.
Dan majalisar ya nuna shakku kan ƙawancen ‘yan adawa, inda ya ce bai ga alamar nasara a tattare da ƴan PDP, LP da ma jam’iyyar APC da suka koma ADC ba.
Barazanar Korewa
Baya ga wannan dakatarwar, ADC ta yi barazanar cewa za ta iya korar dan majalisar wakilan gaba daya idan ya ci gaba da raina shugabannin jam’iyyar. Sakataren jam’iyyar ya bukaci Abejide da ya daina kalaman batanci ga shugabanni, tare da daina duk wata mu’amala da jam’iyyar APC.
Full credit to the original publisher: Legit.ng – https://hausa.legit.ng











