AC Maiwada: Matashin Bakatsinen Da Ya Shahara A Fannin Hulɗa Da Jama’a A Harkokin Gwamnati
Daga Muhammad Bashir, Muhammad Aliyu Rimaye
Farkon Rayuwa Da Karatu
A cikin taron matasan da ke aiki a ma’aikatun gwamnati a yanzu, musamman a hukumomin tsaro, babu shakka suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa martabar hukumomin. Daga cikin wadannan matasa, akwai Assistant Comptroller of Customs Abdullahi Aliyu Maiwada, wanda a halin yanzu shi ne Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙasa (National PRO) a Hukumar Kwastam ta ƙasa (NCS).
AC Maiwada, wanda bai kai shekaru 40 ba, ya kasance abin misali ga matasa masu hazaka da kwarewa a fagen shugabanci. A matsayinsa na kakakin hukumar, yana wakiltar Hukumar Kwastam cikin basira, yana amfani da dabarun zamani na Public Relations don inganta martabar hukumar da kuma gina kyakkyawar alaka da al’umma.
Nasarori Da Kyaututtuka
A ƙarƙashin jagorancinsa, Sashen Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kwastam ya samu kyaututtuka irin su WCO Meritorious Award na shekarar 2024 da Kyautar Mafi Ƙwazo a Fannin Yada Labarai daga NIPR a shekarar 2025. Bugu da ƙari, a shekarar 2023, kamfanin dillancin labarai na Image Merchant Limited ya ba shi Kyautar Kakakin Hukuma Mafi Cancanta.
Tarihin Iyali Da Asali
Duk da shahararsa a matakin ƙasa, da yawa ba su san cewa ɗan Jihar Katsina ne ba. An haife shi a Karamar Hukumar Katsina kuma yana da zuriyar ilimi da shugabanci. Mahaifinsa, Alhaji Aliyu Maiwada, farfesa ne a Jami’ar Bayero, yayin da kakansa, Alhaji Abubakar Maiwada, ya kasance babban malami a fannin Ilimi na Musamman tun shekarun 1960.
A bangaren mahaifiyarsa, AC Maiwada ya fito ne daga zuriyar sarauta. Kakan mahaifiyarsa, Muhammad Gidado, shi ne ɗan fari ga Sarkin Katsina, Sarki Dikko. Wannan zuriyar ce ta haifi Muhammad Salisu (Nalado), wanda ya kasance babban masanin tarihi a masarautar Katsina.
Karatu Da Aiki
Abdullahi Aliyu Maiwada ya fara karatunsa na firamare a Staff Primary School Kano (1992-1997), sannan ya ci gaba da sakandire a Government Science Secondary School Dutsin-Ma. Ya samu digiri na farko a fannin Geography Education daga Jami’ar Bayero, Kano, sannan ya yi digirin digirgir a Environmental Management a shekarar 2011.
Bayan haka, ya samu wani digiri a Mass Communication da Media Arts daga Crescent University Abeokuta, kuma yana ci gaba da karatun PhD a Jami’ar Tarayya, Abuja.
Tun lokacin da ya shiga Hukumar Kwastam a shekarar 2011, AC Maiwada ya rike mukamai daban-daban. Ya fara aiki a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a a Kaduna (2013-2017), sannan ya yi aiki a Jihar Ogun (2017-2020), kafin a naɗa shi Wakilin Hukumar Kwastam a tashar NBCN. A shekarar 2022, an ɗaga shi zuwa Mataimakin Kakakin Hukumar na Ƙasa, kuma a shekarar 2023, ya zama Cikakken Kakakin Hukumar.
Ƙwarewa Da Kyaututtuka
AC Maiwada memba ne na ƙungiyoyin ƙwararru da dama ciki har da Nigerian Institute of Public Relations (NIPR), African Public Relations Association (APRA), da Association of Communication Scholars and Professionals of Nigeria (ACSPN).
Ƙarshe
Wannan matsahin Bakatsinen, wanda ya fito daga tsatson ilimi, ya cancanci yabo da goyon baya daga dukkan Arewacin Najeriya. A yau, idan aka yi maganar sabbin jagorori masu shugabancin Najeriya, babu shakka AC Maiwada yana cikin fitattun matasa da suka cancanci amincewa.
Source: Daily Feeds











