Fitattun Jaruman Kannywood Mata 12 Da Suka Yi Aure Daga 2022 Zuwa 2025

Fitattun Jaruman Kannywood Mata 12 Da Suka Yi Aure Daga 2022 Zuwa 2025

Spread the love

Fitattun Jaruman Kannywood Mata 12 Da Suka Yi Aure Daga 2022 Zuwa 2025

Kano – Masana’antar Kannywood ta kasance daya daga cikin manyan masana’antu a Arewacin Najeriya da ke taka muhimmiyar rawa wajen yada al’adu da nishadantar da al’umma.

Jaruman Kannywood mata 12 ne suka yi aure tsakanin 2022 zuwa 2025
Hoton Aisha Humaira, Rahama Sadau da Maryam Malika a wurare daban-daban. Hoto: Instagram

A cikin shekaru hudu da suka gabata (2022-2025), jarumai mata goma sha biyu daga masana’antar Kannywood sun shiga cikin aure, inda shekarar 2022 ta kasance mafi yawan auren jarumai tare da bakwai daga cikinsu.

Shekarar 2022: Lokacin Aure a Kannywood

1. Aisha Aliyu Tsamiya

Aisha Aliyu Tsamiya ta yi aure a ranar 25 ga Fabrairu, 2022
Tsohuwar jarumar Kannywood, Aisha Aliyu Tsamiya. Hoto: Instagram

A ranar 25 ga Fabrairu, 2022, fitacciyar jarumar Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya ta ba masoyanta mamaki da auren sirri da ta yi ba tare da sanarwar kowa ba. Auren ya gudana a asirce, ba tare da gayyata ko taron jama’a ba.

Tsamiya ta dade tana boye bayanan mijinta har sai daga baya aka gano cewa Alhaji Buba Abubakar ne angonta.

2. Hafsat Idris (Barauniya)

Hafsat Idris Barauniya ta yi aure a ranar 26 ga Fabrairu, 2022
Hafsat Idris a wani taro. Hoto: Instagram

Kamar yadda Tsamiya ta yi, mawakiya Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya ta yi aurenta a asirce a ranar 26 ga Fabrairu, 2022. Auren ya haifar da jita-jita cewa ta auri dan gidan Abacha, wanda ta musanta daga baya.

Duk da tabbatar da cewa ta yi aure, Hafsat ta ki bayyana wanda ta aura har sai da auren ya mutu a 2025.

3. Hassana Muhammad

Hassana Muhammad da Abubakar Bashir Maishadda sun yi aure a 2022
Hassana Muhammad da mijinta Maishadda. Hoto: Instagram

A ranar 13 ga Maris, 2022, jaruma Hassana Muhammad ta yi aure da fitaccen furodusa Abubakar Bashir Maishadda a masallacin Juma’a na Murtala a Kano. Auren ya samu halartar manyan jaruman masana’antar.

4. Ummi Rahab

Ummi Rahab da Lilin Baba sun yi aure a 2022
Ummi Rahab da mijinta Lilin Baba. Hoto: Facebook

A ranar 13 ga Yuni, 2022, jaruma Ummi Rahab ta yi aure da mawaki Abdulrahman Muhammad (Lilin Baba). Auren ya ja hankali sosai saboda shaharar mutanen biyu a masana’antar.

5. Amina Lawan (Raliya Dadin Kowa)

Jarumar shirin Dadin Kowa, Amina Lawan, ta yi aure a karshen Yuli, 2022 a masallacin Juma’a na Old BUK da ke Kano. Auren ya samu halartar manyan abokan aikinta da mahaifiyarta wacce kanta jaruma ce.

6. Rukayya Dawayya

Rukayya Dawayya da Isma'il Na'abba Afakallah sun yi aure a 2022
Rukayya Dawayya da mijinta Afakallah. Hoto: Instagram

Fitacciyar jarumar Kannywood Rukayya Dawayya ta yi aure da Sama’ila Na’abba Afakallah (tsohon shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano) a masallacin Tinshama da ke Kano a 2022.

7. Halima Yusuf Atete

Halima Atete ta yi aure a 2022
Halima Atete da mijinta Muhammad Kalla. Hoto: Facebook

A karshen Nuwamba, 2022, jaruma Halima Atete ta yi aure da dan kasuwa Alhaji Muhammad Kalla a Maiduguri. Bikin ya samu halartar manyan jaruman Kannywood kamar Ali Nuhu da Ahmad Bifa.

2023: Shekarar Auren Rashida Mai Sa’a

8. Rashida Mai Sa’a

Rashida Mai Sa'a ta yi aure a 2023
Rashida Mai Sa’a a lokacin shirye-shiryen aurenta. Hoto: Instagram

A ranar 11 ga Nuwamba, 2023, jaruma Rashida Adamu Abdullahi ta yi aure da Alhaji Aliyu Adamu (Sardaunan Matasan Gwoza) a Unguwar Mallam Bello da ke Daurawa, Kano.

2024: Zawarcin Mansura

9. Mansura Isah

A watan Yunin 2024, tsohuwar matar jarumi Sani Musa Danja, Mansura Isah, ta sake yin aure. Aminiyar jarumar Samira Ahmed ce ta tabbatar da labarin a shafinta na Instagram.

2025: Fitattun Auren Jarumai

10. Aisha Humaira

Auren Aisha Humaira da Dauda Kahutu Rarara
Aisha Humaira da Dauda Kahutu Rarara suna rawa a bikinsu. Hoto: Facebook

A ranar 25 ga Afrilu, 2025, jaruma Aisha Humaira ta yi aure da mawaki Dauda Kahutu Rarara a masallacin Juma’a na Maiduguri. Bikin ya samu halartar manyan mutane kamar Sanata Barau Jibrin da tsohon gwamnan Katsina Aminu Masari.

11. Maryam Malika

Maryam Malika da Abdul M Shareef sun yi aure a 2025
Maryam Malika da mijinta Abdul M Shareef. Hoto: Facebook

A ranar 27 ga Yuni, 2025, jaruma Maryam Malika ta yi aure da jarumi Abdul M. Shareef a masallacin Sani Zangon Daura da ke Kaduna.

12. Rahama Sadau

Rahama Sadau ta yi aure a 2025
Rahama Sadau a gidanta bayan aurenta. Hoto: Instagram

A watan Agusta, 2025, fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure da Ibrahim Garba a Kaduna. Auren ya gudana a asirce har sai da hotunan suka fito bayan daurin aure.

Ce-Ce-Ku-Ce Game da Auren Jaruman Kannywood

Auren jaruman Kannywood na yawan haifar da jita-jita da ce-ce-ku-ce, musamman game da irin bukukuwan da ake yi da kuma kudaden da ake kashewa. Har ila yau, mutane kan yi bincike kan rayuwar jaruman kafin aure don neman aibobi.

Full credit to the original publisher: Legit.ng – https://hausa.legit.ng/kannywood/1669626-rahama-sadau-da-jarumai-mata-da-suka-yi-aure-daga-2022-zuwa-2025/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *