Kwankwaso Zai Iya Maye Gurbin Buhari – Jigon NNPP Ya Bayyana Dalilin

Kwankwaso Zai Iya Maye Gurbin Buhari – Jigon NNPP Ya Bayyana Dalilin

Spread the love

Kwankwaso Ne Zai Maye Gurbin Buhari – Jigon NNPP Ya Fadi Dalilin

Jigo A Jam’iyyar NNPP Ya Bayyana Kwankwaso A Matsayin Mai Iya Maye Gurbin Buhari

Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Alhaji Aminu Ringim, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne ɗan siyasa da zai iya maye gurbin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Jigon NNPP ya ce Kwankwaso zai maye gurbin Buhari
Jigon NNPP ya ce Kwankwaso zai maye gurbin Buhari. Hoto: @MBuhari, @KwankwasoRM (Twitter)

Alhaji Aminu Ringim ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja, a ranar Talata, bisa rahoton jaridar Leadership.

Meyasa Kwankwaso Zai Iya Maye Gurbin Buhari?

Jigon NNPP ya bayyana cewa Kwankwaso yana da halaye da ɗabi’u irin na marigayi Buhari, musamman ma game da kare hakkin talakawa da kuma ƙaunar ƙasa.

“Tabbas giɓin da Buhari ya bari ba mai sauƙin cikewa ba ne, amma idan akwai wani a cikin ƴan siyasar Najeriya da ke ɗauke da amana, ƙanƙantar kai da ƙaunar talakawa irin na Buhari, to babu wanda ya kai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.”

– Alhaji Aminu Ringim

Ya kara da cewa Kwankwaso ya tabbatar da kansa a matsayin ɗan siyasa mai mutane, wanda ke rayuwa tare da jama’a, yana magana da harshensu, kuma yana fahimtar buƙatunsu.

Kwankwaso Na Da Magoya Baya A Duk Faɗin Arewa

Alhaji Ringim ya yi iƙirarin cewa Kwankwaso yana da tasiri a siyasa har fiye da jihar Kano, inda ya ce yana da magoya baya a jihohin Katsina, Jigawa, Zamfara, Sokoto, Kebbi har ma da wasu sassa na Arewa ta Tsakiya.

Kwankwaso ya samu yabo daga wajen jigon NNPP
Kwankwaso ya samu yabo daga wajen jigon NNPP. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso (Facebook)

“Abin da ya bambanta shi da saura shi ne, kwarjininsa ya wuce addini, ƙabila. Ba kawai gwarzon Arewa ba ne, amma mutum ne da ke kan hanyar zama jajirtaccen dattijon ƙasa.”

– Alhaji Aminu Ringim

Ya yi watsi da masu ƙoƙarin takaita Kwankwaso ga siyasar jiha ko yanki, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙaramar fahimta da ba ta dace da tasirinsa a fagen siyasa ba.

Majalisa Za Ta Karrama Buhari

A wani labarin kuma, majalisar dattawan Najeriya ta shirya karrama marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Majalisar za ta gudanar da wani taron karramawa na musamman a ranar Laraba, 24 ga watan Yulin 2025, domin girmama marigayin shugaban ƙasa.

Karramar ta zo ne bayan rasuwar Buhari a wani asibiti a birnin Landan a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.

Asali: Legit.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *