Malamin Jami’a Ya Yi Mafarkin Shugaba Buhari Ya Shiga Aljanna

Daura, Katsina – Wani malamin jami’a a jihar Yobe, Sheriff Almuhajir, ya bayyana cewa ya yi mafarkin ganin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin Aljanna. Bayanin ya zo ne bayan an binne marigayin shugaban a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.
Mafarkin Da Ya Jawo Cece-Kuce
Almuhajir, wanda kwararre ne a fannin ilimin addinin Musulunci a jami’ar Yobe, ya bayyana mafarkin ne a shafinsa na Facebook inda ya rubuta: “Wallahi na yi mafarkin Buhari ya shiga Aljannah.”
Martanin da bayanin ya jawo ya kasance daban-daban, inda wasu suka amince da mafarkin yayin da wasu kuma suka nuna shakku kan gaskiyarsa.
Goyon Bayan Masu Bi
Daga cikin masu goyon baya, Imam Sani ya ce: “Allah ya tabbatar. Ameen. Kuma kaima Allah yayi maka ƙarshe mai kyau da sakamakon Aljannah.”
Wani mai suna Ibrahim Aliyu Tahir ya kara da cewa: “Ya Allah ka yafe mana gaba ɗayan mu. Kowa mai laifi ne. Idan ba ka yafewa Buhari ba, to ka daina zagin shi.”
Masu Shakku Kan Mafarkin
A gefe guda, wasu sun nuna shakku kan gaskiyar mafarkin. Abban Adawiyya Alharazumy ya ce: “Wannan shi ake kira da rudani. Kaima kasan karya ka gani kawai.”
Muhammad Aliyu ya kara da cewa: “Mafarki kala-kala ne kuma ba kowane mafarki ne gaskiya ba. Wani mafarkin magagin barci ne.”
Amina Mohammed Ta Yaba Wa Buhari
A wani lamari na daban, mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed, ta yaba wa marigayi Buhari. Ta bayyana cewa shugaba Buhari ne ya karfafa mata gwiwa wajen tafiya aiki majalisar dinkin duniya.
Hajiya Amina ta ce akwai darussa da dama da ‘yan Najeriya za su koya a rayuwar marigayi shugaban, inda ta kira shi “mutumin kirki mai himma ga al’umma.”
Buhari Ya Rasu A London
Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, a birnin London bayan fama da rashin lafiya. An kai gawarsa Najeriya a ranar Talata kuma an binne shi a gidansa da ke Daura bisa ka’idojin addinin Musulunci.
Jana’izar ta kasance cikin sauki kamar yadda shugaban ya yi wasiyya, inda shugaban kasa Bola Tinubu da wasu manyan jiga-jigan gwamnati suka halarta.
Martanin Jama’a
Bayan bayyana mafarkin, jama’a sun yi ta ra’ayoyi daban-daban a shafukan sada zumunta:
- Lawan Alhaji Umaru: “Allah ya tabbatar da hakan. Wannan ba komai ba ne a wajen Mahaliccin mu mai iko da komai.”
- Aisha M. Kazimiyyah: “Idan ka ci nama kafin barci, kana iya mafarkin kana ci. Ina addu’a Allah ya saka a makoma ɗaya da Buharin.”
Kamar yadda aka saba, mafarkai kan manyan mutane na jawo cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman idan sun shafi shugabanni da suka rasu.
Asali: Legit.ng











