2027: Dino Melaye Da Wasu Manyan Abokan Atiku Sun Bar PDP Domin komawa ADC

2027: Dino Melaye Da Wasu Manyan Abokan Atiku Sun Bar PDP Domin komawa ADC

Spread the love

Dino Melaye Da Wasu Na Hannun Daman Atiku Sun Fice Daga PDP Zuwa ADC

Abuja – Kawancen ‘yan adawa a Najeriya na kara samun karfi karkashin jagorancin Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi. A ranar 16 ga Yulin 2025, Atiku ya fice daga jam’iyyar PDP, inda ya bayyana cewa akwai sabani da ba za a iya warwarewa ba tsakaninsa da jam’iyyar.

2027: Dino Melaye Da Wasu Manyan Abokan Atiku Sun Bar PDP Domin komawa ADC
Dino Melaye yana tare da Atiku Abubakar a wani taron siyasa. Hoto: @atiku/Twitter

Shirin Atiku Na Zaben 2027

Ko da yake Atiku yana cikin hadakar da ta kaddamar da ADC, amma bai sauya sheka zuwa jam’iyyar ba a hukumance. Tun kafin ya bar PDP, jam’iyyar da ya tsaya mata takarar shugaban kasa a zabukan 2019 da 2023, Atiku tare da ‘yan adawa sun ayyana ADC a matsayin jam’iyyar hadakarsu.

Wasu daga cikin abokan siyasar Atiku sun bi sahun ficewarsa daga PDP. A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta gano wasu manyan mutane uku daga cikin na hannun daman Atiku da suka sauya sheka zuwa ADC.

Na Hannun Daman Atiku Da Suka Koma ADC

1. Sanata Dino Melaye

Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ajiye katin shaidarsa ta zama dan PDP, inda ya zargi jam’iyyar da gazawa wajen zama babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

A wata wasikar murabus da ya aika wa shugabancin PDP, Dino Melaye ya ce ba zai iya ci gaba da shiga ayyukan jam’iyyar ba. A cikin wasikar, ya bayyana cewa:

“Na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP daga yau. Wannan mataki ya zama dole saboda jam’iyyar ta rasa karfi da damar ceto ‘yan Najeriya daga halin da ake ciki.”

Bayan haka, Melaye ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X (Twitter), inda ya rubuta: “SDM Fully ADC,” wanda ke nuna ya shiga sabuwar jam’iyyar hadaka.

2. Aliyu Bello

Aliyu Bello, sakataren kudi na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, ya ajiye mukaminsa sannan kuma ya fice daga jam’iyyar. Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Alhaji Aliyu Bello ya koma ADC domin shirye-shiryen zaben 2027.

Alhaji Aliyu, wanda ya shafe dogon lokaci a PDP kuma amini ne ga Atiku, ya aika da wasikun murabus guda biyu a ranar Laraba, 16 ga Yuli, 2025 – daya zuwa shugaban PDP na jihar Kaduna, daya kuma zuwa shugaban PDP na mazabarsa.

3. Hon. Musa Elayo Abdullahi

Tsohon karamin ministan shari’a kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben Atiku na 2023, Musa Elayo, ya fice daga PDP bayan shekara 26 da kasancewa a jam’iyyar.

Ya aike da wasikar murabus dinsa mai dauke da kwanan wata 10 ga Yuli, 2025 zuwa ga shugaban PDP da sakataren mazabarsa. A wasikar, Elayo ya bayyana cewa:

“Na yanke wannan shawarar ne bayan zurfin tunani da nazari dangane da akidun siyasa da manufofi na.”

Bayan ficewarsa daga PDP, tsohon ministan ya kuma sanar da komawarsa jam’iyyar hadaka ta ADC.

‘Yan Takarar Gwamna Sun Bar PDP Zuwa ADC

A wani labarin, tsofaffin ‘yan takarar gwamna a Ondo, Eyitayo Jegede da Agboola Ajayi, sun fice daga jam’iyyar PDP a hukumance. Eyitayo Jegede da Cif Agboola Ajayi yanzu sun shiga haɗakarsu Atiku Abubakar da ke neman kalubalantar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Sauran manyan jiga-jigan da suka sauya sheƙa zuwa ADC sun haɗa da tsohon sanatan Ondo ta Kudu, Nicholas Tofowomo, kamar yadda suka bayyana a wani taro a Ondo.

Asali: Legit.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *